Tinubu na kwana da tunanin talakawan kasa - Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jaddada aniyar shugaba Bola Tinubu na ba da fifikon jin dadin rayuwa ga dukkanin ‘yan Nijeriya kamar yadda suke a cikin shirye-shirye da manufofin gwamnatinsa.

Mataimakin shugaban kasan ya bayyana haka ne a ranar Litinin din nan a wajen bikin kaddamar da rabon kayan abinci na Naira biliyan 5.1 da gwamnatin jihar Sokoto ta yi ga masu karamin karfi domin rage radadin cire tallafin man fetur. 

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu shugaba ne mai tausayi wanda yake kwana da kuma tashi kowace rana da tunanin yadda zai rage wa ‘yan Nijeriya halin da suke ciki musamman marasa karfi a cikinmu" inji Shettima.

Post a Comment

Previous Post Next Post