Ba mu saba doka ba don mun murtsuke baburan Okada a Abuja - Hukuma

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa a babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja, ta ce murtsuke baburan yan Okada da ta yi ba saba doka ba.

Deborah Osho, shugabar aiyuka a hukumar ta DRTS ce ta bayyana hakan a wata hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Lahadi.

Kamfanin na dillancin labarai na NAN ya bada wani rahoto a ranar 31 ga watan Agustan da ya gabata na yadda hukumar ta kama tare da murtsuke babura guda 400 na yan acaba da aka samu da laifin gudanar da aiki ba bisa ka’ida ba a birnin na Abuja.

Post a Comment

Previous Post Next Post