Zaben shugaba mai nagarta na kara wa kasa kima a idon duniya inji Dr Sirajo Yakubu


Kwararren lauya a Nijeriya Dr Sirajo Yakubu Batagarawa na da ra'ayin cewa kasashe masu tasowa na iya kai wa duk inda ba su tsammani ta fuskar ci gaba, muddin suka rika zabar mutane masu nagarta a wajen shugabanci.

Dr Sirajo Yakubu Batagarawa wanda shi ne shugaban Sashen Koyon Aikin shari'a da Aikin Lauya na Kasa-da-Kasa a  Jami'ar Nile, Abuja na magana ne a taron masana kan siyasa, tattalin arziki da yakar miyagun laifuka a Jami’ar Cambridge da ke kasar Ingila a lokacin da ya ke gabatar da makala mai taken: Kima da Mutunci (Integrity).

Malamin jami'ar ya ce akwai bukatar a yaki cin hanci da rashawa da karfin tuwo, muddin ana so a samar da ci gaba mai dorewa a cikin kasa, inda ya kara da cewa babu kasar da za ta ci gaba, matukar cin hanci ya yi mata katutu.

Da ya koma ta fuskar siyasa kuwa, kwararren lauyan ya ce akwai bukatar a tsaftace siyasa musamman a kasashe masu tasowa daga banga da sara-suka da kage da cin mutuncin juna ta yadda za ta zamo abin koyi na kwarai ga matasa masu tasowa.

Ya ce akwai bukatar kasashe masu tasowa da su tashi tsaye wajen yaki da bambancin addini, bangaranci ko al'ada, ta yadda hadin kansu zai ba su damar kawo ci gaba mai ma'ana ga kasarsu don su amfana.

A bangaren kafafen yada labarai kuwa, Dr Sirajo Yakubu Batagarawa ya shawarce su da su ba da gudunmuwa yadda ya kamata wajen yaki da cin hanci da rashawa ganin irin tabon da aikata hakan ke jazawa ga kima da martabar wadanda aka samu da aikata laifin.

Post a Comment

Previous Post Next Post