Jagoran babbar jam’iyyar adawa ta LUMANA Afirka a Nijar Hama Amadou ya dawo gida
Tun a farkon mulkin hambararren Shugaba Bazoum, Hama Amadou ya bar Nijar daga cikin gidan fursuna bayan hukuncin da kotu ta yanke masa kan badakalar safarar jarirai.
Duk da cewa Hama Amadou ya samu sauki, wasu na zarginsa da tsawaita zamansa a Faransa a maimakon ya dawo Nijar ya ci gaba da zaman kaso. To sai dai babu tabbas ko jagoron na LUMANA zai wuce gidan kaso ya ci gaba da zaman hukuncin da aka yanke masa ko kuma a’a.