Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya nada dan cikinsa David Kudakwashe Mnangagwa mukamin karamin minista bayan sake zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasar.
Wannan nadi dai ya tayar da kura a siyasar kasar, inda wasu ke zargin shugaban kasar da nadin 'yan'uwa da abokan arziki a gwamnatinsa.
An nada David Kudakwashe Mnangagwa mai shekaru 34 a mukamin karamin ministan kudi a yayin da aka nada Tongai Mafidhi, da ga dan'uwan shugaban a matsayin karamin ministan shakatawa na kasar.
Emmerson Mnangagwa dai ya ayyana sunayen mutane 26 da ya nada mukaman ministoci a sabuwar gwamnatin.
A shekarar 2017 dai ne aka fara zaben Mnangagwa mai shekaru 80 a matsayin kasar Zimbabwe.