Wani matashi mai suna Ridwan dan kimanin shekaru 20 a duniya ya hallaka mahaifinsa domin ya yi tsafin da zai sa ya samu kudi a jihar Ogun.
Kungiyar 'yan sintirin jihar Ogun dai ne suka yi nasarar kama matashin a yankin Ijebu ta arewa a jihar. Kwamandan sintirin Soji Ganzallo a cikin wata sanarwa ya ce jami'ansa ne suka yi nasara kama matashin a lokacin da suke aikin sintiri, sai suka ji hayaniyar mutane a cikin wani kango.
Ganzallo ya ce da jami'ansa suka kutsa kai cikin gini, sai suka tarar da mutum sharbe cikin jini, wanda ake zargin ya yi aika-aikar ya tsere.
Kwamandan ya ce nan take ya ba jami'ansa umurnin su kamo wanda ake zargin cikin sa'o'i 24, kuma haka aka yi, suka nemo shi a inda ya ke labe a cikin daji.