Barayi sun zane masu gadi sun yi awon gaba da kadarorin N20m a Jigawa

Wasu da ake kyautata zaton barayi ne sun afka ma'aikatar samar da ruwan sha a garin Birnin Kudu da ke karamar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa, inda suka lakada wa ma’aikata duka tare da sace wasu kayayyaki na sama da Naira miliyan 20.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Ibrahim Garba ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyar a ranar Juma’a.

Garba, wanda ya nuna damuwarsa kan lamarin, ya ce gwamnati za ta dauki tsauraran matakai kan masu yin zagon kasa ga kokarinta na samar da ruwan sha ga mazauna jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post