Kudin Aikin Hajjin 2024 sun tunkari N5mHukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya  NAHCON ta bukaci maniyyata da ke son gudanar da ibadar aikin Hajj a shekarar 2024 da su saka mafi karanci kudin da suka kai Naira miliyan 4.5,  inda ta bayyana cewa aikin hajji mai zuwa zai yi tsada.


Shugaban Hukumar NAHCON, kuma Babban Jami’in Hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya Talata a Abuja

Hukumar ta kuma yi nuni da cewa ana duba rahotannin kwamitocin na aikin Hajjin bana na 2023 da ya gudana.


Ya ce tuni hukumar ta fara kaddamar da shirye-shiryen domin tunkarar yadda za a yi aikace-aikacen maniyyata da ke son yin Aikin Hajjin shekarar 2024

2 Comments

  1. Allah ya kawomana Amma gaskiya an tdaowalama talaka dauki

    ReplyDelete
Previous Post Next Post