Kotu ta hana NNPP dakatar da Kwankwaso


 

Alkalin Babban Kotun Jihar Kano Mallam Usman Na'abba ya jingine dakatarwar da jam'iyyar NNPP tsagin Dr. Boniface Aniebonam ta yi wa tsohon gwamnan Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso. Kazalika alkalin kotun ya dakatar da Dr. Boniface da 'yan tawagarsa daga bayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar har sai an kammala shari'a. Alkali Usman Na'abba ya kuma bukaci hukumar zabe ta INEC da ka da ta yi mu'amula da wadannan mutane a matsayin shugabannin jam'iyyar NNPP.

Wannan hukuncin dai ya biyo bayan karar da aka shigar a gaban kotun ne bayan dakatarwar da su Dr. Boniface din suka yi wa Kwankwaso a ranar 29.08.2023. Sai dai kuma jaridar Punch wacce ta ruwaito wannan labari na jingine dakatarwar Kwankwaso ba ta bayyana ko matakin ya shafi korar da shugabannin na NNPP suka yi wa jagoran Kwankwasiyya daga jam'iyyar a wannan Talata ba. A ranar 05.10.2023 kotun za ta ci gaba da sauraran wannan kara da ke a gabanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp