Mai dokar barci: 'Yan sanda sun sace babur din 'yan fashi a Ghana


 Jami’an tsaro a birnin Tamale na arewacin Ghana sun kama wasu ‘yan sanda guda biyu da laifin sace babur din wasu ‘yuan fashi da aka kama.

Tun farko ‘yan sandan sun sacewa wasu ‘yan fashi babur din ne bayan da bude wuta a dai-dai lokacin da wata kotu take gab da yanke hukuncin fashi da makami da ake zargin abokin su da aikatawa.

Tuni dai aka tsare yan sandan biyu da suka hadar da Lance Copral Muhammad Aboagye da Sergent Elvis Emmanule, inda kuma aka bude kundin bincike akan su.

A bincike farko-farko da jami’an tsaro suka gudanar sun gano cewa dai-dai lokacin da ‘yan sandan ke musayar wuta da mutanen bayan sun bude wa kotun wuta, a lokacin ne su kuma ‘yan sandan suka zagaya bayan kotun inda masu laifin suka ajiye ababen hawan su ba tare da wata-wata ba kuma suka yi awon gaba da mashin din.

Bayan bincike da kama mutanen 13 ne kuma suka gane mashin din su a lokacin da ake hole su a shalkawatar rundunar ‘yan sandan kasar, kuma ba tare da bata lokaci ba, suka shaidawa jami’an tsaro cewa wannan shine mashin din su da aka sace.

Jaridar Ghanian Times ta ruwaito cewa tuni aka adana mashin din a shalkawatar rundunar ‘yan sandan kasar, yayin da aka fara bincike don gano sauran Babura 3 da ‘yan fashin suka ce an sace musu.

Post a Comment

Previous Post Next Post