DSS ta kama wasu mutane da ake zargi da karkatar da tallafin da gwamnatin tarayya ta bayar don rabawa jama'a


Hukumar tsaron sirri ta DSS a Najeriya ta sanar da kama wasu mutane da hannu a karkatar da kayayyakin abincin da gwamnatin tarayya ta samar don rabawa jama’a.

Hukumar ta ce duka mutanen da ta kama jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa NEMA ne, kuma mafi yawan su an kama su ne a kasuwar Lafia da ke jihar Nasarawa lokacin da suke tsaka da sayar da kayan ga ‘yan kasuwa.

Mai Magana da yawun hukumar Peter Afunanya ya ce tuni aka kamo wasu kayayyakin da mutanen suke yunkurin sayarwa.

Afunanya ya kuma bukaci jama’ar Najeriya da su sanya idanu sossai kan masu sayar da kayan abinci don basu rahoton masu sayar da kayan da gwamnati ta tanadar don rabawa jama’a a kyauta.

Haka kuma hukumar ta ce ta kama wasu mutanen na daban wadanda sune suke shirya yadda za’a sace kayan kafin ma a kai su kasuwa.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp