Harin 'yan ta'adda ba zai sare mana guiwar yakar ta'addanci a jihar Katsina ba - Dikko Radda

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya ce hare-haren ta'addanci da 'yan bindiga ke kai wa a yankunan karkarar jihar ba zai sare wa gwamnatinsa guiwa ba ta daina yakarsu.

Malam Dikko Umaru Radda ya sake nanata cewa ba zai yi sulhu da 'yan bindigar ba har sai idan su ne suka ji wuta suka nemi su ajiye makamansu.

Da ya ke magana don murnar cika kwanaki 100 a bisa karagar mulki, Gwamna Radda ya ce gwamnatinsa na nan na daukar matakai daban-daban da za su magance matsalar tsaron jihar.

Ya ce sama da kudi Naira bilyan 7 gwamnatinsa ta kashe don sayo kayan aikin da za a yaki wadannan 'yan ta'adda a jihar. Daga cikin kayan aikin kamar yadda ya ce akwai motoci masu sulke 10 da motoci kirar Toyota Hilux guda 65 sai babura 700 da za a rarraba wa jami'an tsaro su gudanar da ayyukansu.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta kuma dauki matasa 1,500 a karkashin sabuwar cibiyar inganta tsaro ta 'Katsina Community Watch Corp' domin su kare yankunansu. Ya kara da cewa yanzu haka ana horar da su yadda ya kamata.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp