Kotu ta daure mutumin da ya saci lemon kwalba a Adamawa

Wata kotu a jihar Adamawa ta yanke hukuncin daurin watanni 6 ga wani matashi Nafi'u Sabe da aka samu da laifin satar katan 6 na maltina.

An dai yanke masa wannan hukunci bayan da ya amsa laifinsa na satar wannan maltina.

Alkaliyar kotun Hafsat Abdurrahman ce ta yanke wannan hukunci.

Nafi'u Sabe ya amsa laifinsa inda ya ce ya saci wannan maltina ne a kasuwar Jimeta jihar Adamawa a Agustan, 2023, inda ya yi nadamar aikata hakan.

Post a Comment

Previous Post Next Post