Majalisar dokokin jihar Kano ta gayyaci matashin da ya tsinci Naira Miliyan 15 kuma ya mayarwa mai shi


Majalisar dokokin jihar Kano ta gayyaci matashi Auwalu Salisu da ke sana’ar tuka babur din adai-daita Sahu, bayan da ya mayar da wasu makudan kudade har naira miliyan 15 ga wani fasinjan sa dan asalin kasar Chadi.

Wannan na zuwa ne bayan bukatar hakan da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Doguwa Alhaji Salisu Muhammad ya gabatarwa majalisar, yayin zamanta na yau, karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Isma’il Jibril Falgore.

Majiyar DCL Hausa ta Daily Trust ta ruwato cewa matashin  mai shekaru 22 ya mayar da kuddaden ne bayan da fasinjansa ya manta da su a cikin adai-daita sahun sa.

Yayin zaman majalisar, dan majalisa Muhammad ya ce matashin ya nuna tsantsar tawakkali da kuma hali na gari wajen mayar da kudaden idan aka yi la’akari da halin matsin da ake ciki, a don haka ya kamata majalisar ta karrama shi.

Wannan ce ta sa shugaban majalisar ya amince da bukatar, yayin da ya amince a gayyaci matashin sannan yayi alkawarin cewa majalisar zata tallafa masa.

Dukannin mambobin majalisar 44 sun amince da wannan bukata, a cewar su wannan zai karfafawa sauran matasa gwiwa kan su rika sanya gaskiya cikin harkokin su na yau da kullum.

 

 

1 Comments

  1. Masha Allah may Allah bless them for trying to consider him

    ReplyDelete
Previous Post Next Post