Kungiyar marubutan da ke kare hakkin bil'adama ta HURIWA ta zargi shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu da nada mukamai a tsakanin 'yan'uwa da aminnan arzikinsa kadai, inda kungiyar ta yi zargin cewa yana nada muhimman mukaman ne daga 'yan kabilar Yarabawa.
Kungiyar ta yi wannan zargin ne a cikin wata sanarwa daga babban jami'inta Emmanuel Onwubiko, inda sanarwar ta yi magana kan nadin Gwamnan babban bankin kasa CBN da shugaban hukumar tattara kudin haraji ta FIRS da Shugaba Tinubu ya yi a kwana-kwanan nan, da ya nada duk Yarabawa.
Kungiyar ta bukaci shugaba Tinubu da kada irin layin da tsohon shugaban kasa Buhari ya bi wajen irin wadannan mukamai.