Gwamnan Edo ya umurci a kulle ofishin mataimakinsa, bayan rikicin siyasa da ke tsakaninsu

Rikicin siyasa na ta kara ruruwa tsakanin Gwamnan Edo da mataimakinsa

Da sanyin safiyar Litinin din nan, mataimakin Gwamnan jihar Edo Philip Shaibu ya tarar da an kulle kofar shiga ofishinsa a gidan gwamnatin jihar.

Dama dai an dade ana takun-saka tsakaninsa da Gwamna Godwin Obaseki ta dalilin wanda zai gaje shi a zaben 2024 na Gwamnan jihar.

Shaibu Philip dai ne mataimakin Obaseki tun 2016, da bayanai ke cewa yana son a bashi takarar Gwamna a 2024 idan wa'adin Obaseki ya kare, yayin da shi kuma Gwamna Obaseki ke da wanda yake son ya gaje shi.

Mataimakin Gwamnan dai ya zargi gwamnan da yunkurin tsige shi daga mukaminsa, dalilin da ya sa har sai da jiga-jigan jam'iyyar PDP a jihar suka sa baki batun ya kwaranye.

Wannan sa'in-sa dai ce ta ci gaba, har ta kai ga an fitar da ofishin mataimakin Gwamnan ya zuwa wani kango da ba a kammala ginawa daga wajen gidan gwamnati.

Da sanyin safiyar Litinin din nan kuma mataimakin Gwamnan ya kama hanyar zuwa ofishinsa, ya tarar an kulle kofar shiga.

Post a Comment

Previous Post Next Post