Zafin kishi ya sa wani saurayi ya bugi budurwarsa har ya karyata a Kano


Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a ofishin hukumar Hisbah a Kano ta tsare wani saurayi Abbas Sadiq bisa zarginsa da karya budurwarsa bayan da ya same ta tana waya da wani saurayi daban.

Ana tuhumar Abbas Sadiq mazaunin Unguwar Sheka da laifuka uku da suka hada da hana 'yancin dan'adam, amfani da karfi da kuma ji ma wani rauni.

'Yan sandan sun sanar da kotu cewa budurwar ta ce musu haka kawai saurayin ya hau ta da bugu har ya karya mata hannu bayan da ya same ta tana waya da wani saurayin.

Da aka karanta masa laifukan, nan take ya amsa. Alkalin kotun Khadi  Sani Tanimu Sani Hausawa ya umurci da a cigaba da tsare shi a gidan gyaran hali har sai ranar 25 ga watan Agusta da za a sake zama.

Post a Comment

Previous Post Next Post