'Yan sanda sun hallaka dan ta'adda sun kwato tumakin sata a Katsina

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta sanar da kashe wani dan ta'adda daya tare da kwato tumakin sata 60 a wata musayar wuta tsakaninsu da 'yan ta'adda a kauyen Kogoro na yankin Daddara ta karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Kazalika rundunar 'yan sandan ta ce ta kuma yi nasarar kwato bindiga samfurin AK-47 da kuma alburusai 110.

A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ASP Aliyu Abubakar Sadiq, ta ce 'yan sandan sun samu labarin 'yan ta'addar sun durfafi kauyen Kogoro na yankin Daddara ta karamar hukumar Jibia a jihar Katsina, inda suke harbi na kan mai uwa da wabi suka sace tumaki. Da jin haka, DPO na karamar hukumar Jibia ya tattara jami'an 'yan sanda suka far musu, aka yi musayar wuta. Da suka ji matsi ne suka watsar da wadannan dabbobi suka yi kokarin ranta a na kare. Bayan nan ne 'yan sanda suka gano tumakin nan 60 da gawar dan ta'adda da bindiga da alburusai.

ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya ce yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Post a Comment

Previous Post Next Post