Jagoran PDP A Jihar Katsina, Shema Na Shirin Shiga Jam'iyyar APC

Tsohan gwamnan jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, ya shirya tsaf domin barin jam'iyyarsa ta PDP zuwa jam'iyyar APC nan ba da jimmawa.

Barista Ibrahim Shehu Shema ya ziyarci shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a gidansa da ke Abuja a daren jiya Asabar a cigaba da Shirye-shiryen shigarsa jam'iyyar APC.

Majiyarmu ta shaida mana cewa Shirye-shirye sun kammala na karɓar jagoran jam'iyyar PDP a jihar Katsina kuma jigo a matakin Kasa, Alhaji Ibrahim Shehu Shema zuwa APC.

Alhaji Ibrahim Shehu Shema ya yi gwamnan jihar Katsina daga shekarar 2007 zuwa 2015 kuma shi ne jagoran jam'iyyar PDP a jihar Katsina.

Post a Comment

Previous Post Next Post