Barr Hannatu Musawa na da kwarewa da gogewar da duk ake bukata wajen gina kasa - Alhaji Abdullahi Yaya


Wani dan kishin kasa daga jihar Katsina Alhaji Abdullahi Umar Yaya ya yaba wa shugaban kasa Bola Tinubu da ya dauko Barr Hannatu Musawa domin nada ta matsayin minista kuma mamba a majalisar zartarwa ta kasa.

Abdullahi Umar Yaya ya ce duba da gida da tsatson da Barr Hannatu ta fito, da yadda mahaifinta marigayi Musan Musawa ya yi ta fadi tashin ganin an yi jagoranci na adalci a cikin al'umma tun zamanin su Malam Aminu Kano da cigaban talakawa ke zukatansu.

Ya ce Barr Hannatu ta cimma nasarori daban-daban a lungu da sako na jihar Katsina kuma ta kafa tarihin zama mace ta farko da aka nada matsayin mukamin minista daga jihar Katsina.

Alhaji Abdullahi Umar Yaya ya ce irin gogewa da kwarewar da Barr Hannatu ke da ita ya sa duniya ke mutuntata har shugaban kasa ya ga ya dace a ba da sunanta daga jihar Katsina don nada ta mukamin minista.

Kwararriya a aikin lauya, Barr Hannatu Musawa na da rajin kare hakkin bil'adama, sannan tana da burin ganin matasa sun samu sana'o'in hannu domin dogaro da kansu, sannan tana sha'awar rubuce-rubuce domin inganta ilmi.

Dan kishin kasar ya ce irin wadannan halaye na Barr Hannatu Musawa ne wasu matan da ma mazan ke kwaikwaya domin su kyautata wa al'ummarsu.

Ya yi godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya zabi Barr Hannatu Musa Musawa a matsayin daya daga cikin 'yan majalisar zartarwa ta kasa. Hakan ya nuna yadda shugaba Tinubu ke da adalci a tsakanin jinsi.

Alhaji Abdullahi Umar Yaya ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya saci zuciyar Katsinawa musamman matasa da ya yi wannan kyakkyawan zabi na Barr Hannatu Musawa daga jihar Katsina.

Post a Comment

Previous Post Next Post