Wani Bakano ya raunata yaro don ya hana shi bashin koko da kosai


Kotun shari'ar musulunci a karamar hukumar Kiru ta jihar Kano ta tsare wani mutum mai suna Jaafar Lukman bisa zarginsa da raunata wani yaro dan wata mata Jamila Mai Kosai da ke sayar da koko da kosai, don sun hana mutumin bashin koko da kosai.

Kazalika, kotun ta yi zargin mutumin ya sa kafa ya harbe bokitin koko da kaskon suyar kosan da kuma kwanon da ake ajiye kosan matar a saman titi a lokacin da takaddamar ta barke.

'Yan sanda sun ce bincikensu ya gano cewa mutumin ya tafi wajen matar ne da nufin ta ba shi bashin koko da kosai, amma dai matar ta hana saboda ta ce tana binsa bashin wasu kidin da bai biya ba.

Bayan ta hana shi ne ya sa kafa ya harbe bokitin kokon da kaskon suyar kosan har man ya yi buja-buja a kasa.

Lokacin da aka karanto masa laifukan da ake zarginsa da aikatawa, mutumin ya amsa, amma ya sanar da kotu cewa a lokacin ransa ne ya baci, Kasantuwar yana jin yunwa a lokacin.

Alkalin kotun, Khadi Usman Haruna Usman ya dage zaman sauraron shari'ar sai 4 ga watan Satumba, sannan ya umurci a ci gaba da tsare mutumin a gidan gyaran hali.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp