Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da nadin Barr Abdullahi Garba Faskari a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar.
Abdullahi Garba Faskari dai shi ne tsohon mataimakin Gwamnan jihar Katsina Barr Ibrahim Shema a wa'adi na biyu na mulkin jihar Katsina daga 2011 zuwa 2015 da ya maye gurbin Arch Ahmad Musa Dangiwa da ya samu mukamin minista a Abuja.
Kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun Gwamna Radda, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, ta ce nadin ya fara aiki ne nan take.
Tun a watan Maris na 2019 dai Abdullahi Garba Faskari ya bar jam'iyyar PDP ya koma APC.
Ya dai rike mukamin babban lauyan gwamnati wato Attorney General a jihar Katsina daga 2003 zuwa 2007 zamanin Marigayi Malam Umaru Musa Yar'adua. Sannan bayan Gwamna Shema ya hau wa'adin farko na mulkinsa a jihar Katsina ma Abdullahi Garba Faskari ya ci gaba da rike mukamin kwamishinan shari'a na jihar daga 2007 zuwa 2009, inda ya bar ma'aikatar shari'a ya koma kwamishinan ilmi daga 2009 zuwa 2010.