'Yan bindiga sun kai wa jami'an 'yan sanda hari a Zamfara


'Yan Bindiga Sun kai hari a ofishin 'yan sanda na karamar hukumar Bundugu a jihar Zamfara, sun kuma hallaka tare da jikkata mutane.

Wata majiya ta shaida wa jaridar LEADERSHIP cewa gungun ‘yan bindigar da sun boye kansu a gonaki da ke kusa da inda suka kai farmaki a  ofishin ‘yan sanda.

Majiyar ta ci gaba da cewa wani jami’in dan sandan ya rasa ransa sakamakon artabu da ‘yan sandan suka yi da ‘yan bindigar.

Sai dai majiyar ta DCL Hausa ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, inda ya bayyana cewa basu da masaniya kan  harin, amma ya ce zai tuntubi baturen ‘yan sanda (DPO) da ke karamar hukumar Bungudu domin jin cikakken bayani.

Post a Comment

Previous Post Next Post