Jaridar Katsina City News ta sauya suna zuwa Katsina Times Newspaper

Mawallafi kuma mallakin jaridar nan ta yanar gizo mai suna Katsina City News Malam Danjuma Katsina na sanar da jama'a cewa ya sauya sunan jaridar zuwa Katsina Times Newspaper.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Malam Danjuma Katsina, mamallakin jaridar ya ce hakan ya zamo wajibi domin cimma duk wasu tsare-tsare da za su sa jaridar ta zamo tsara a idon duniya ba kamar sunan Katsina City News ba da aka takaita a Katsina kadai ba.

Sanarwar ta ce za a iya samun dukkanin wallafe-wallafen da suka gabata ta shafin www.katsinatimes.com.

Malam Danjuma Katsina ya ce sun yi karatu a tsanake sun gano cewa akwai kasashe kusan 29 da ke da jaridu da ke amfani suna kusan makamancin wannan irinsu Khaleej Times da ke kasar Qatar, Tehran Times da ke kasar Iran, Istanbul Times da ke kasar Turkiyya da New York Times da ke kasar Amurka.

Sauran su ne Japanese Times ta kasar Japan, Hindustan Time ta kasar Indiya, Daily Times, Premium Times da ke a Nijeriya sai kuma yanzu da aka samu Katsina Times, ita ma a Nijeriya.

Mawallafin ya sanar cewa ya dakatar da wallafa a jaridarsa ta 'The Links News' domin kara yawan ma'aikata a jaridar Katsina Times. Ya kara da cewa tuni sun cimma yarjejeniya da wasu Editoci na manyan jaridun duniya domin dillanci da musayar labarai tsakaninsu da jaridar Katsina Times, inda Katsina Times za ta rika ba su labaran jihar Katsina, Nijeriya da ma nahiyar Afrika, su kuma za su rika ba ta labaran sauran sassan duniya.

Za a dai rika wallafa jaridar da Turanci da Hausa domim ta ilmatar, fadakar da nishadantar da masu karatu.

Post a Comment

Previous Post Next Post