Tinubu zai binciki ayyukan bankin CBN

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya shaida cewa ba da jimawa zai fara bincike mai zurfi kan ayyukan bankin kasa na CBN.

Kazalika, shugaban kasar ya ce gwamnatinsa za ta yi garambawul ga aikin gwamnati da kuma gudanar da bincike mai zurfi kan tsarin biyan albashin ma'aikatan.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngelale, inda ya rawaito shugaban kasar ya fadi haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban bankin duniya Mr Ajay Banga.

Post a Comment

Previous Post Next Post