Za mu tabbatar an daina kasa kayan sana'a a bisa titunan jihar Katsina - Kwamandan KASSAROTA

Sabon Kwamandan hukumar kula da ababen hawa da tabbatar da dokar tuki ta jihar Katsina KASSAROTA Comr Amiru Tsiga ya sanar cewa za su yi aiki tukuru don tabbatar da mutane sun daina baza baza sana'o'i a bisa titunan da aka ware don mutane da ababen hawa su wuce.

Comr Amiru Tsiga na magana ne a lokacin da shiga ofis a matsayin sabon Kwamandan hukumar a Katsina.

A ranar 21 ga watan Agusta, 2023 ne dai Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da nadin Manjo Yahaya Rimi mai ritaya a matsayin Darakta Janar da Amiru Tsiga a matsayin Kwamandan hukumar ta KASSAROTA.

Hukumar KASSAROTA dai ce ke da alhakin kula da ababen hawa da yanayin tuki da kuma tabbatar da ba a zuba kayan kasuwa a kan titunan da mutane ke amfani da su ba da sauran ayyukan tsaftace harkar tuki.

Amiru Tsiga ya ce batun kasa kayan sana'a a bisa titi ya dade yana ci masa tuwo a kwarya tun kafin a bashi wannan mukami. Don haka ne ya ce zai ba da tashi gudunmuwa sosai don ganin an rika amfani da titi yadda ya dace.

Kwamandan ya ce ayyukan hukumar KASSAROTA ya shafi har ma wanda bai da wani abin hawa, madamar dai zai yi amfani da titin da aka tanadar don al'umma su bi, ko a kafa ko a keke.

"Ni gaskiyar magana, yana daya daga cikin abin da ke min tuwo a kwarya, tun kafin Allah Ya kawo ni wannan matsayin. Kuma ina kira ga su masu ababen hawa, hukumar KASSAROTA ba wuri bane na cutar da al'umma a jihar nan. Mutane ne kamar kowa, illa kiran da zan yi, al'ummar jihar Katsina su bi doka da oda".

Ya yi godiya ga Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda da ya ba shi damar hidimta wa al'ummar jihar ta hanyar nada shi wannan mukami da ya ce zai yi amfani da shi domin al'ummar jihar su amfana.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp