Wani mahaukacin kare a birnin Osogbo na jihar Osun ya yi sanadiyyar mutuwar wata jaririya 'yar watanni biyar da haihuwa.
Mahaifiyar jinjirar Nafisat Muideen ta ce lokacin da lamarin ya faru a cikin rukunin gidajen Hallelujah babu wadanda za su kai mata daukin gaggawa.
Mahaifiyar jinjirar ta ce lamarin ya faru da misalin karfe 1:45 na rana a lokacin da take kan hanyar zuwa shago don sayo wa diyar magani.
Ta ce tana cikin tafiya ta ji haushin kare a bayanta, juyawarta ke da wuya, karen ya yi tsalle ya cimma yarinyar da ke goye a bayanta.