"Za mu kara albashin ma'aikatan Shari'a don yaki da rashawa" - Tinubu


Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi alkawari cewa gwamnatinsa za ta yi wa ma'aikatan Shari'a karin albashi da ma sanya masu alawus-alawus ta yadda za a magance matsalolin cin hanci da rashawa a fannin Shari'a.

Shugaba Tinubu ya yi wannan alkawarin ne yayin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A cewar sanarwar shugqban ya ce sun lura cewa ya zama tilas gwamnati ta yi yaki da cin hanci da rashawa don haka za su yi nazari sosai kan albashi da alawus-alawus na jami'an shari'a".

Tawagar NBA ta samu jagorancin shugaban kungiyar, Yakubu Maikyau, babban lauyan Nijeriya (SAN), mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale.

Post a Comment

Previous Post Next Post