'Yan ta'adda sun sace jigon APC a Kaduna


'Yan ta'adda sun sace Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC, a jihar Kaduna Hon Kawu Ibrahim Yakasai a gidansa da ke kauyen Yakasai na karamar hukumar Soba ta jihar a daren Juma'a.

Daily Trust ta rawaito cewa 'yan ta'addar sun kutsa kai gidan mutumin da misalin karfe 10 na daren Juma'a, inda suka yi awon gaba da shi zuwa wani wurin da har yanzu ba a kai ga sani ba.

Hon Kawu Ibrahim Yakasai dai tsohon shugaban karamar hukumar Soba ne ta jihar Kaduna.

Lawal Shehu, mai magana da yawun Gwamnan jihar Kaduna ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce Gwamna Uba Sani ya umurci jami'an tsaro da su durfafi 'yan ta'addar nan su kuma tabbatar sun kubutar da Hon Yakasai.

Post a Comment

Previous Post Next Post