'Yan Nijeriya sun yi ''wawa'' a wajen rabon kayan tallafi

Wasu mutane a jihar Bayelsa da ke Najeriya sun fasa tare da wawushe rumbun tara hatsi da sauran kayan abinci da gwamnatin jihar ta killace a birnin Yenagoa domin raba wa jama’a da zummar rage radadin ibtila’in ambaliyar ruwa tun a 2022. 

RFI Hausa wacce ta ruwaito wannan labarin ta ce gwamnatin jihar ta ce wasu daga cikin kayan abincin sun fara lalacewa. 

An fasa rumbun ne da ke kan babbar hanyar Isaak Boro a Yenagoa saboda irin tashin hankalin da al’umar ke ciki na hauhawar farashn kayayyakin masarufi wanda ya samo asali daga cire tallafin man fetur da ya haddasa tsananin tsadar rayuwa. 

Janye tallafin ne ya sa farashin man fetur  ya yi tashin goron-zabi daga N190 zuwa 620 kan kowacce lita wanda hakan ya shafi farashin motocin sufuri da kayan abinci da sauransu.

Sai dai Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Bayelsa ta bayyana cewa wadannan kayayyakin abincin da aka kwashe ba su da ingancin da za a iya aci, domin sun lalace don haka duk wanda ya ci zai fuskanci matsala. 

PUBLICITÉ

Post a Comment

Previous Post Next Post