Tinubu ya haramtawa wasu mukarraban gwamnati zuwa Amurka

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya haramtawa jami’an gwamnati wadanda basu da alaka ta kai tsaye da taron majalisar dinkin duniya zuwa wajen taron.

Shugaba Tinubu ya bada umarnin a dakatar da Shirin karbar Visar da ake yiwa jami’an gwamnatin wadanda babu wata gudumowa da zasu bayar idan sun halarci taron.

Kakakin shugaban Ajuri Ngelale ta cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce wannan na cikin kokarin da gwamnatin shugaba Tinubu ke yi na rage kashe kudade baji ba gani da gwamnati ke yi.

Sanarwar ta kuma kara da cewa an dorawa ministoci da manyan shugabannin hukumomin gwamnati da su sanya idanu wajen ganin ma’aikatan su basu tafi Amurka wajen taron ba matukar dai basu da abin yi a wajen.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post