Uganda ta zartas da hukuncin kisa kan matashin da aka samu da auren jinsi


Mahukuntan kasar Uganda sun yankewa mutum na farko hukuncin kisa a tarihin kasar, bayan kama shi da laifin take dokokin da suka haramta auren jinsi.

Wannan shi ne karo na farko da kasar ta zartas da hukuncin da take ikirarin dauka duk da yadda kasashen yammacin duniya suka yi watsi da wannan mataki.

Dokar dai ta tanadi daurin rai da rai idan aka kama mutane biyu da laifin auren jinsi, sannan ta tanadi hukuncin kisa kai tsaye idan aka sake kama su a karo na biyu, ko kuma suka yiwa wani irin wannan dabi’a ta dole har ya kamu da cuta, ko kuma tilastawa karamin yaro ko tsoho ko masu bukata ta musamman.

Rahotanni sun ce tuni aka zartas da hukuncin kisan kan matashin mai shekaru 20, bayan an same shi da laifin maimaita luwadin bayan kamun da aka yi masa na farko da wani mutum mai shekaru 41.

Tuni dai shugaban kasar dama ‘yan majalisa suka fara shan suka, kan wannan mataki da suka dauka, wanda ake ganin yana da matukar tsauri.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp