Mahukuntan jihar Uttar Pradesh ta India sun rufe wata makaranta mai zaman kanta, bayan da aka sami rahoton wata Malama da ta umarci daliban ta su mari abokin karantu su, kawai saboda kasancewar sa musulmi.
Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta ce bayan bullar Labarin dalibin da aka mara, bincike ya tabbatar da cewa makarantar mai suna Neha bata cika ka’idojin koyo da koyarwa ba.
Bayanai sun ce tuni aka fara kokarin rarraba daliban a tsakanin marantun gwamnatin da ke yankin.
Tun farko malamar mai suna Tripta Tyagi ta umarci daliban ta su bi layi su kuma yi ta dallawa wa dalibin dan ajin su mari kawai saboda kasancewar sa musulmi.
Sai dai a ganawar Malamar da kafar yada labarai ta NDTV ta ce bata dana sanin abinda ta aikata, sai dai ta musanta cewa ta yi hakan ne don addinin dalibin, sai don bai yi aikin gida da ta bashi ba.
To amma ba tun yau ba iyayen yaron sun sha yin korafin cewa yaron yana yawan gaya musu malamar tana dukan sa da kuma aibata addinin sa.
A Wani gajeran Faifan bidiyo da ya rika yawo a karshen mako ya nuna yadda Malamar ta Umarci daliban su bi layi tare da marin abokin karatun nasu dan shekaru 7, kuma an jiyo lokacin da take musu tsawa cewa “Me yasa kuke marin sa a hankali? Ku mare shi da karfi”
Haka kuma an jiyo lokacin da take cewa “ku dake shi a baya yanzu fuskarsa ta yi ja” yayin da yaron ke tsaye yana kuka.