Faransa ta haramtawa mata musulmai sanya Hijabi a cikin makarantu


Gwamnatin kasar Faransa ta haramtawa mata Musulmai amfani da Hijabi, abaya ko kuma rufe kan su a cikin makarantu.

Tuni dai wannan sabuwar doka ta fara cin karo da suka daga kungiyoyin kare hakkin addinai da dai-daikun mutane, duk da cewa gwamnatin kasar ta ce ta yi haka ne don kare mata Musulman.

Wannan na zuwa ne bayan da cin zarafi da kuma kyamar mata musulmai ke kara ta’azzara a kasar da  ta yi kaurin suna wajen kyamatar addinin musulunci

Ta cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta ce mata musulmai a kasar na fuskantar kyara, tsokana da kuma cin zarafi musamman a tsakanin abokan karatun su da malamai a cikin makaratu, a don haka hana su sanya Hijabi ko kuma rufe gashin su ne kadai hanyar da zai sa su saje da sauran dalibai da nufin gujewa cin zarafi.

Sanarwar ta kuma kara da cewa bai kamata a ce da zarar malami ya shiga aji ya gane daliba musulma da wadda ba musulma ba.

Tun ba yanzu ba, malamai a kasar sun sha yin korafin cewa gane banbanci tsakanin daliban su musulmai da wadanda ba musulmai ba, yana hana su gudanar da aikin su yadda ya dace saboda irin ba banbancin mu’amala da ke tsakanin mabanbantan addinan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp