Shugaba Tinubu ya karbi goron gayyatar tattaunawa da Joe Biden na Amurka


Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya amince da tayín ganawar da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi masa, a gafen taron majalisar dinkin duniya.

Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada Labarai, Aguri Ngelale ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, jim kadan bayan kammala ganawar shugaban na Najeriya da babbar jami’ar diplomasiyyar Amurka kan nahiyar Africa Molly Phee.

Sanarwar ta kunshi cewa shugaba Tinubu ya kuma jadadda cewa ya zama wajibi Najeriya ta yi zarra a bangaren kasuwanci da jayo masu zuba jari a karkashin mulkin sa.

Bayan amsa tayin ganawar da shugaban Biden, Tinubu ya kuma bukaci Amurka ta taimakawa Najeriya ta hanyar  habbaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

A nata bangaren jami’ar ta Amurka kan Hulda da nahiyar Africa Uwargida Phee  ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen ganin alaka ta kyautatu a tsakanin Najeriya da kasar Amurka.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post