Garin kwaki ya yi ajalin wata budurwa a Kano

 Wata Budurwa mai suna Fiddausi Mahmud da ke garin Rimin Hamza a karamar hukumar Tarauni a jihar Kano ta mutu a sakamakon cin  garin kwaki da ta yi wanda ake zargin ya kulle mata ciki  lokacin da take matsananciyar jin yunwa.

Gidan rediyon Rahama da ke Kano ya ruwaito cewa mahaifin Fiddausi, Malam Mahmud Abdullahi ya ce iyalansa sun kwashe tsawon yini guda ba samu abincin da za su ci ba abin da ya sa ya fita nema kuma ya yi dace ya samo musu garin kwaki. Magidancin ya ce ba ya samun abin da ya wuce Naira 500 a rana guda, lamarin da ya kara jefa rayuwar iyalansa cikin wani mayuwacin hali la'akari da tsadar rayuwar da ake fuskanta a Nijeriya bayan janye tallafin man fetur.

Rahotanni sun ce tuni aka yi janaizar marigayiya Fiddausi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

1 Comments

Previous Post Next Post