'Yan majalisa na son gwamnati ta yaki cutar 'malaria' da karfin tuwo

Kwamitin majalisar wakilan Nijeriya kan cutar sida, tarin fuka da cutar zazzabin cizon sauro ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kafa dokar ta baci kan cutar malari duba da irin hatsarin da ke tattare da cutar.

Shugaban kwamitin Amobi Godwin Ogah ya sanar da hakan a ranar yaki da cutar malari ta duniya.

Ya ce duba da irin hatsarin da cutar ke da shi ya ga ya dace gwamnati ta dauki dukkanin matakan da suka kamata don magance matsalar da yakar sauron da ke haddasa ta.

Amobi Godwin ya bukaci gwamnatoci daga dukkanin matakai da su bullo da tsare-tsaren da za su fatattaki sauro a cikin al'umma.

Dan majalisar ya ce kwamitin zai yi aikinsa ta hanyar bibiyar cibiyoyin kiwon lafiya na yankunan karkara don gani da ido yadda hukumomin kula da lafiya daga tushe ke aiwatar da aikin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da alkinta shirin Roll back Malaria.

Post a Comment

Previous Post Next Post