Nijeriya na bin bashin kudi Naira bilyan 132.2 ga kwastomomin kasashen ƙetare a Nijar da Togo da Benin na kudin lantarkin da suka sha na tsawon shekaru hudu.
Kididdigar kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, ta nuna cewa ana bin wadannan kasashen wannan bashin ne tun daga shekarar 2018 har zuwa rubu'in farko na wannan shekara ta 2023.
Hukumar da ke lura da harkokin lantarki ta Nijeriya NERC ta fitar da jadawalin yadda aka raba wutar ga kasashen, inda ta ce an biyo kasashen bashi ne bayan da aka caje su kudin lantarki Naira bilyan 180.8, a yayin da su kuma suka biya Naira bilyan 48.57, kaso 26.8% kenan suka iya biya.
Kididdigar ta nuna cewa an fi bin kasar Benin kaso mai tsoka na kudin, inda ake binta, Naira bilyan 72.1 sai kasar Nijar da ake bi Naira bilyan 31.3 da kasar Togo da ake bi Naira bilyan 10.03.