Ana zanga-zanga a Kano


Zanga-zanga ta barke a Kano duk da haramcin hakan da 'yan sanda suka yi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Kano Muhammad Usain Gumel ya haramta wata zanga-zanga da magoya bayan jam'iyyar NNPP da na APC suka bukaci mambobin su da su fito su yi a jihar.

Zanga-zangar dai ta biyo bayan zargin bayar da cin hanci ga sashen shari'a na jihar ya yi ba daidai ba game da batun shari'ar  zaben gwamna na 2023.

Kwamishinan ya ce duk wani yunkurin aiwatar da wannan zanga-zanga, zai zamo wata kafa ta kawo tsaiko ga tsaron kasa.

Sai dai kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, jim kadan bayan fitar da wannan sanarwa, masu zanga-zangar suka yi fitar farin dango, suka cike titunan jihar suka nufi gidan gwamnatin jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post