Gwamna Uba Sani ya zabtare kudin rajistar manyan makarantun jihar Kaduna

 


Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya sanar da rage kudin rajistar shiga manyan makarantun jihar, a wani mataki na rage tsadar rayuwar da ke addabar jama'a ciki har da Kaduna. Sanarwar da DCL Hausa ta samu a kan wannan batu ta nuna cewa yanzu kudaden rajistar makaratun jihar sun koma kamar haka:

Jami'ar Jihar Kaduna 

- Kudin makarantar sun koma 105,000 a maimakon N150,000

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli 

- Kudin makarantar sun koma N50,000 a maimakon N100,000

Kwalejin Kiwon Lafiya ta Shehu Idris Makarfi

-HND: N70,000 a maimakon N100,000
-ND: 52,000 a maimakon N75,000

Wannan na zuwa ne a kwanaki kalilan bayan da wasu mata a jihar ta Kaduna suka yi zanga-zangar tsadar rayuwa.


Post a Comment

Previous Post Next Post