Matar da yunwa ta kusa yi wa lahani a Katsina ta samu kabakin arziki


Matar nan mai suna Hadiza Abubakar da ke zama a birnin Katsina da ta kwashe kwanaki kusan 9 ba ta ci abinci ba, ita da 'ya'yanta, ta samu tallafin kudi tsaba har Naira milyan 7 daga al'umma a sassan kasar nan daban-daban.

Malama Hadiza 'yar asalin jihar Kwara, ta zo Katsina da zama bayan da mijinta dan asalin Giwa, jihar Kaduna ya zo da ita. Bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce mijin ya gudu ya barta, babu abinci. Tana fita nemar wa 'ya'yanta abin da za su ci ne, wani mai babur ya banke ta, har ta ji raunin da ba za ta iya fita neman abinci ba.

Wannan dalilin ne ya sa ta kwashe kwana kusan 9 ba su ci abinci ba, ita da 'ya'yanta, dalilin da ya sa masana kiwon lafiya suke ganin kamar yunwa ta kama matar da 'ya'yanta.

Bayan banke ta da babur ne, wasu makwabtanta, suka je domin yi mata "kamu" a inda ta ji raunin, a nan ne suka fahimci halin da take ciki har wani matashi mai suna Ahmad Abdullahi BilHaqqi ya yi mata bidiyo ya tura a kafar sadarwar zamani domin nemar mata taimako. Dalilin da ya sa bidiyon ya karade ko'ina har aka samu wannan tallafi. 

Bayan nadar bidiyonta ne suka garzaya da ita asibitin Turai Yar'adua, Katsina domin ceto ranta. Sai dai daga bisani aka mayar da ita asibitin kwararri na Medical Center, Katsina.

Da yake yi wa manema labarai karin haske a Katsina matashin da ya wallafa bidiyon matar, Ahmad Abdullahi BilHaqqi, ya ce mutane sun bayar da gudunmuwa sosai daga sassa daban-daban na kasar nan.

Ya ce mutane sun ba da gudunmuwar kudi da ta kayan abinci da yanzu haka ake da buhunan shinkafa 7 manya da kanana 6.

Kazalika akwai wake buhu da masara da Taliya da Indomie da man girki da 'kwamaso' da sauran kayan abinci iri daban-daban.

Ahmad Abdullahi BilHaqqi ya ce an samu wannan tallafi ne kasa da kwanaki uku da aka fitar da sanarwar neman taimakon.

Matashin ya ce za su saya mata gida da kudin kuma su ba ta jarin da za ta rika sana'ar da za ta rike kanta da yaranta hudu, biyu maza, biyu mata.
Ahmad Abdullahi BilHaqqi ya ce sun kira taron manema labarai ne domin a sanar da al'umma yawan tallafin da aka samu kuma gwamnati ta daukin nauyin hidimomin matar. Ya kara da cewa su na sanar da mutane da su daina turo da wata gudunmuwa, don bata-gari na amfani da lambar bankin su na zamba-cikin aminici.

Daga cikin kungiyoyin da suka shige gaba don ba da tallafin da kuma ganin al'umma sun tallafa, akwai kungiyar Katsinawa ta HOHDI da ta Shagari Low Cost Community Development da kungiyar da 'yar gwagwarmaya Fauziyya D Sulaiman da ke Kano ke jagoranta da sauransu.

1 Comments

Previous Post Next Post