Ya zama dole mu yi karin albashi - Sabon ministan Kwadago

 
Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyar ta na magance matsalolin rayuwa ga ma'aikatan kasar ta hanyar bullo sabon mafi karancin albashin ma’aikata da sauran abubuwan jin dadi da zai kawo magance wahalar rayuwa da suke ciki sakamakon cire tallafin man fetur.

Simon Lalong, sabon ministan kwadago da samar da ayyukan yi ya yi wannan alkawarin a lokacin da yake karbar mukaminsa a ranar Litinin a Abuja.

Lalong ya ce hakan ya zama wajibi domin bunkasa kyakkawar alaka tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyoyin kwadago na NLC da kuma TUC.


Post a Comment

Previous Post Next Post