'Yan bindiga sun hallaka jami'an kwastam a jihar Kebbi

Hukumar kwastam ta tabbatar da mutuwar jami'anta guda biyu bayan wata musayar wuta tsakanin jami'an nata da wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne kan titin Bunza-Dakingari-Koko a jihar Kebbi.

A cikin wata sanarwa daga Jami'in hulda da jama'a na hukumar ta kwastam a jihar Kebbi Mubarak Mustapha da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da jami'an ke aikin binciken ababen hawa, 'yan bindigar a cikin wata mota samfurin Toyota Corolla suka far musu, su kuma suka mayar da biki, aka ci gaba da musayar wuta, har aka samu wannan asarar rayuka.

Sanarwar ta ce jami'an da suka rasu sun hada da Alhaji Kabiru Shehu mai mukamin 'Insfekta' da Abdullahi Muhammad mai mukamin 'Custom Assistant' da sanarwar ta ce tuni an rigaya an yi musu sutura.

Yanzu haka dai hukumar kwastam din ta kaddamar da farautar wadanda suka yi wannan aika-aika da zummar kama su don girbar abin da suka shuka.

Kwantarolan hukumar a jihar Kebbi Ben Oramalugo ya yi ta'aziyya ga iyalan mamatan tare da roko ga al'umma da su rika kwastam bayanan sirri ingantattu da za su taimaka a dakile safarar kaya ba bisa ka'ida ba da sauran masu aikata assha a cikin al'umma. 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp