Safarar shanu, tumaki, dabino da sauran kayan bukata da ake shigowa da su Nijeriya daga Jamhuriyar Nijar ta samu tangarda bayan rufe iyakar kasashen biyu.
Nijeriya dai ta sanar da rufe iyakarta da Nijar bayan da soji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Bazoum a watan 26 gaJuli, 2023.
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa kaso mai tsoka na naman shanu da ragunan da ake ci a sassan Nijeriya daban-daban na zuwa ne daga Jamhuriyar Nijar.
Kusan jihohi 6 dai ne suka yi iyaka da Jamhuriyar Nijar da suka hada da Katsina, Jigawa, Yobe, Sokoto, Borno da Kebbi.
'Yan kasuwa da sauran masu safara na kokawa cewa wannan mataki na gwamnatin Tinubu ya tsayar da harkokinsu cik, inda suka yi roko da gwamnati ta sake duba na tsanaki game da matakin.