An yi jana'izar sojoji 20 da aka kashe a Neja

Yanzu an gudanar da jana'izar sojoji 20 da harin 'yan ta'adda ya rutsa da su a jihar Neja.

A makon jiya dai ne hukumomi daga bangaren sojin Nijeriya suka sanar da mutuwar jami'ansu 36, bayan da 'yan ta'adda suka yi musu kwanton-bauna a hanyar  Zungeru-Tegina na jihar Neja a lokacin da suke bisa jirgi.

Daily Trust ta ba da labarin cewa ministocin tsaro Muhammad Badaru da Bello Matawalle da shugaban sojin Nijeriya CG Musa duk sun halarci jana'izar.

Karin wadanda suka halarci jana'izar, sun hada da mataimakin Gwamnan jihar Neja Yakubu Garba da shugaban sojin kasa Taoreeq Lagbaja da sauransu.

Daga cikin wadanda aka yi jana'izarsu akwai Habib Aliyu da ya shiga aikin soji a shekarar 2020 da Nura Muhammad da ya shiga aikin a shekarar 2016 da sauransu.

Post a Comment

Previous Post Next Post