Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayar da umurnin a jami'an tsaro su cafke mutumin da ya mallaki benen nan mai hawa biyu da ya ruguje a daren Laraba a unguwar Garki, Abuja.
Wike ya ba da umurnin a lokacin da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru a ranar Alhamis.
ya kuma bukaci babban sakatare na hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, Adesola Olusade, da ya biya kudaden jinyar wadanda ke kwance a asibiti.