Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da jama'a cewa masara da sauran kayan abinci da ake ta yamadidi cewa an raba a wasu sassan jihar gurbatacci ne, to ba daga gwamnatin jiha bane, daga kananan hukumomin jihar ne.
Kwamishinan yada labaran jihar Malam Bala Salisu Zango ya sanar da hakan a lokacin taron manema labarai a Katsina.
Kazalika, kwamishinan yada labaran ya ce kudin da ake cewa gwamnatin tarayya ta ba jihohi Naira bilyan biyar-biyar, to jihar Katsina Naira bilyan 2 kacal ta samu daga gwamnatin tarayya.
Ya ce "an jawo hankalin gwamnatin jihar Katsina game da wani labari da ke yawo a kafafen yada labarai cewa gwamnatin tarayya ta ba jihohi kudi Naira bilyan biyar-biyar domin samar da ababen saukaka rayuwa. Ina mai farincikin sanar da ku cewa Naira bilyan 2 kacal gwamnatin jihar Katsina ta samu daga gwamnatin tarayya domin sayo hatsin da za a rarraba wa al'ummar jihar."
Ya ci gaba yana cewa "akwai alfanu a fayyace cewa, gwamnatin tarayya ta shirya kashe Naira bilyan 5 domin sayo masara, shinkafa da taki don raba wa ga jihohi, amma sai gwamnoni suka nace cewa sai dai a ba jihohi kudinsu kai tsaye domin su sayo wadannan kayan abinci da taki, domin farfado da tattalin arzikin kananan 'yan kasuwa da saukaka hanyoyin rabon kayan da sauran hanyoyin duk da za a bi don samun sauki wajen aiwatar da shirin. A haka, gwamnatin tarayya ta ba da wadannan kudade ga jihohi."
Babu ko shakka, gwamnatin tarayya ta umurci babban bankin kasa na CBN da ya ba da kudin ga jihohi a matsayin bashi mai saukin 'ruwa', wanda gwamnatin tarayya za ta biya kaso 52% sai jihohi su biya kaso 48% a cikin watanni 12."
Ya ce ya zama wajibi, a nan, a fayyace cewa, gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda PhD ta karbi wannan Naira bilyan 2, har ma ta yi abin da ya dace da ita, ta sayo buhunan shinkafa 40,000 da za a rarraba a runfunan zaben da ke jihar.
Bugu da kari, a kwana-kwanan nan, kwamishinan ya ce, Gwamna Radda ya umurci kananan hukumomi a jihar Katsina da su sayo tare da rarraba masara ga al'umma kyauta a kananan hukumominsu. Ya cigaba yana cewa Gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin a saukaka tsadar rayuwa da al'umma ke fuskanta bayan cire tallafin man fetur.
"An rigaya an sayo wadannan kayan abinci, kuma an rarraba ga al'umma a dukkanin runfunan zaben da ke jihar Katsina."
Kan haka ne, ake kira ga al'ummar jihar Katsina da su kara nutsuwa cike da tabbacin cewa da zarar gwamnatin tarayya ta kara kawo daukin wasu kudin, gwamnatin jihar Katsina za ta kara sayo wasu kayan abincin domin raba wa ga jama'ar yadda ya dace."
Sai dai ya ce wannan masarar marar kyau da ake zargin an raba, kuma ake alakantata da gwamnatin jiha, to ba daga gwamnatin jihar take ba, sai dai daga kananan hukumomi.