Tsageranci ne a sake gurfanar da ni a gaban kotu-Hudu Ari


Dakataccen kwamishinan zaben jihar Adamawa Barista Hudu Ari ya maka kungiyar lauyoyi ta kasar a gaban kotu bayan kishin-kishin din da suke yi na  sake gurfanar da shi a gaban kotu.

 

Ari na wannan barazana ne, bayan da kungiyar ta NBA ta fara  yunkurin sake gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin yunkurin karkatar da sakamakon zabe, bayan karbar na goro.

A cewar Ari babu wata hujja da kungiyar ta ke da ita na sake gurfanar da shi a gaban kotu, kasancewar waccan kotun da aka kai shi ta bada umarnin a tsaya a inda ake har sai ta kammala binciken da ta ke yi.

Ari ya ci gaba da cewa tsageranci ne ga kotu idan suka sake gurfanar da shi kan laifi guda, don haka ya bukace su da kada su kuskura su fara, matukar ba haka ba kuma ta tabbata suma basa mutunta aiki su.

Tun farko dai ana zargin Yunusa Ari da ayyana Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa alhali ba’a ma kammala girka sakamakon zabe ba, dalilin da ya sa aka rika yada jita-jitar cewa ya karbi cin hancin kudade har naira biliyan guda.

Wannan dalili ne ya sa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta sanar da dakatar da shi daga aikin sa sannan kuma aka gurfanar da shi a gaban kotu, sai dai kuma fara shari’ar ke da wuya kotu ta bukaci a dakata har sai an kammala bincike.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp