Abinda na gaya wa Shugaba Tinubu kan ziyarata a Nijar - Abdulsalami Abubakar

Tsohon shugaban Najeriya Abdulsalam Abubakar ya sanar da mikawa shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu rahoto kan batutuwan da suka tattauna yayin ziyarar tawagar da ya jagoranta zuwa jamhuriyar Nijar.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawar sa da shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar ya ce dukkanin alamu sun nuna cewa yaki ba zai shawo kan al’amarin ba, a maimakon haka kamata ya yi a rungumi tattaunawar diplomasiyya.

Ganawar ta su ta sami halarcin shugaban majalisar zartaswar kungiyar ECOWAS Dr Omar Touray da kuma babban mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada labarai Malam Nuhu Ribadu.

Bayan kammala ganawar ta su, shugaban Najeriya Tinubu wanda kuma shine shugaban ECOWAS ya sha alwashin yiwa rahoton Nazari na tsanaki, kafin daga bisani kuma a san matakin da za’a dauka.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ECOWAS ta sanar da cewa ta gama duk wani shiri na fadawa Nijar da yaki.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post