Rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Hadin kai sun sanar
da ceto karin dalibar Chibok guda daya.
Dalibar na cikin daliban Chibok 276 da ‘yan Boko Haram suka yi
garkuwa da su a ranar 14 ga watan Afrilun 2014 a cikin makarantar su da ke
kauyen Chibok na jihar Borno.
Da
yake Karin haske kwamandan rundunar Manjo Janar Gold Chibuisi ya ce bayan likitoci
sun kammala gwaje-gwaje akan dalibar mai suna Mary Nkeki, ya mikata ga hannun
kwamishinan harkokin mata ta jihar Borno Hajiya Zuwaira Gambo. Dalibar mai shekaru
27 ta kubuta daga hannun Boko Haram din ne tare da mijinta wanda shi dan Boko
Haram ne amma ya mika kai ga rundunar sojin mai suna Adamu. Bayanai sun nuna cewa sojojin sun yi nasarar gano Mary da
mijinta ne akan iyakar Najeriya da Kamaru a kokarin da suke yi na guduwa daga
sansanin ‚yan Boko Haram din, bayan da mijinta ya kuduri aniyar ajiye makamin
sa. Kafofin yada labaran Najeriya sun ruwaito cewa
Mary ta haifi yara guda biyu, sai dai sun mutu a sakamakon matsanaciyar cutar
yunwa da ta kama su lokacin da suke cikin dajin Gulumba dake karamar hukumar
Bama ta jihar Borno.